Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yara kimanin dubu 700 sun kamu da cutar COVID-19 a Amurka
2020-10-15 14:59:37        cri
Kungiyar fasahar jinyar yara da kungiyar asibitocin yara na kasar Amurka, sun fidda sabon rahoto cikin hadin gwiwa, inda suka bayyana cewa, bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19, ya zuwa yanzu, yara kimanin dubu dari 7 sun kamu da cutar a kasar Amurka. Kana, cikin 'yan kwanakin nan, adadin yara da suka kamu da cutar ya karu cikin sauri, har adadin ya kai dubu 80 cikin makwanni biyu da suka gabata.

Cikin rahoton, an yi cikakken bayani kan yaran da suka kamu da cutar a sassan kasar Amurka. An ce, ya zuwa ranar 8 ga wata, yara guda 697,633 sun kamu da cutar, adadin da ya kai kaso 10.7% na jimillar wadanda suka harbu da ita. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China