Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Biden ya lashe zaben Amurka yayin da Trump ya ki amincewa da shan kaye
2020-11-08 15:21:00        cri
Dan takarar jam'iyyar Demokrat Joe Biden ya lashe zaben shugabancin Amurka na 2020 a daren Asabar, yayin da abokin hamayyarsa Donald Trump ya ki amincewa da shan kaye a zaben.

A jawabin murnar lashe zaben da ya gabatar daga birnin Wilmington na jahar Delaware, Biden ya bukaci a hada kai kana ya yi kiran kai tsaye ga magoya bayan Trump, yayin da kasar ke fuskantar baraka a siyasance da rarrabuwar kawunan jama'a dake cigaba da karuwa.

Tun da farko, shugaba Trump ya bayyana zaben na 2020 a matsayin mai cike da magudi, har ma ya yi ikirarin kalubalantar zaben a gaban shari'a.

Jawabin mista Biden na zuwa ne 'yan sa'o'i kadan bayan hasashen da kafafen yada labaran Amurka suka yi na lashe kujerun wakilan zabe sama da guda 270.

A rahoton da gidan talabijin na Amurka ya watsa, sama da Amurkawa miliyan 74 ne suka kada kuri'unsu ga mista Biden, yayin da wasu mutanen sama da miliyan 70 suka jefawa Trump nasu kuri'un, lamarin dake nuna alamun samun baraka a kasar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China