Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ta shirya tattaunawa da Rasha kan yarjejeniyar rage makamai
2020-10-21 14:07:41        cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta fitar da wata takaitacciyar sanarwa a jiya, inda ta ce Amurka ta yabawa kudirin kasar Rasha na ganin an samu ci gaba kan batun rage makaman nukiliya, kuma a shirye Amurkar ta ke ta gaggauta tattaunawa tare da Rasha don cimma yarjejeniyar rage makamai da za a iya bincikar ta.

A jiya ne kuma, ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta fitar da sanarwa cewa, Rasha ba ta samu amsa daga kasar Amurka kan shawarar Rasha ta tsawaita wa'adin sabuwar yarjejeniyar rage makamai bisa manyen tsare-tsare a kalla tsawon shekara daya ba. Rasha tana shirya yin alkawari a siyasance tare da kasar Amurka wato kiyaye yawan makaman nukiliya na kasashen biyu a cikin wa'adin da aka tsawaita domin samun amsar kasar Amurka kan batun. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China