Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Biden ya sha gaban Trump a wasu muhimman jahohi 4 yayin da ake shirin fara zabe
2020-11-02 09:49:40        cri
Dan takarar jam'iyyar Demokarat a zaben neman shugabancin kasar Amurka Joe Biden ya sha gaban shugaban kasar Donald Trump, wanda ke yiwa jam'iyyar Republican takara, a wasu muhimman jahohin kasar hudu, kamar yadda alkaluman hasashen ra'ayoyin masu zabe suka nuna a ranar Lahadi, kwanaki biyu gabanin ranar zaben kasar.

Hasashen ra'ayoyin masu zaben, wanda jaridar New York Times da Siena College suka gudanar tsakanin ranar 26 zuwa 31 ga watan Oktoba ya nuna cewa, Biden, tsohon mataimakin shugaban kasar, a halin yanzu yana samun galaba kan abokin hamayyarsa Trump a jahohin Wisconsin, Pennsylvania, Florida da Arizona.

Trump wanda ya yi nasara kan Hillary Clinton a dukkan jihohin hudu a zaben shekarar 2016, ya yi nasarar a jihohin Wisconsin da Pennsylvania ne da kasa da maki guda. Faduwarsa a daya daga cikin wadannan jihohin zai iya baiwa mista Biden yiwuwar samun nasarar lashe zaben kasar.

Kawo yanzu Biden yana gaban mista Trump da maki 3, inda ya samu kashi 47 yayin da Trump ke da kashi 44 bisa 100, a mafi yawan yankunan jihar Florida, akwai babbar tazara kamar maki 3.2, kamar yadda alkaluman suka nuna. A shekarar 2016, Trump ya lashe jahohi mafiya hadari da maki 1.2.

A jahar Pennsylvania, inda can ne aka haifi Biden, dan jam'iyyar ta Demokarat mai hamayya ne ke kan gaba da maki 6, inda ya samu kashi 49 yayin da Trump ke biye masa da kashi 43 bisa 100, an samu banbancin maki 2.4 a tsakaninsu, kamar yadda alkaluman suka nuna. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China