Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran ta musanta tsoma baki cikin zaben shugaban Amurka
2020-10-26 10:03:53        cri

Majalisar kula da kundin tsarin kasar Iran, ta yi watsi da zarge-zargen da ake wa kasar, dangane da yin katsalandan a zaben shugaban Amurka dake karatowa.

Kakakin majalisar, Abbas Ali Kadkhodaei, ya ce Iran ta sha nanata cewa, ba ta tsoma baki cikin harkokin gidan kasashe. Baya ga haka, ba ta ga amfanin yin hakan ga zaben Amurka ba.

Ya kara da cewa, zaben shugaban kasar batu ne na cikin gidan Amurka, wanda Iran ba ta da niyya ko bukatar shiga.

Jawabin na jami'in martani ne ga furucin daraktan hukumar tattara bayanan sirri na Amurka John Ratcliffe ya yi a baya-bayan nan, wanda ya zargi Iran da Rasha da samun bayanan masu kada kuri'a, a wani yunkuri na kawo tsaiko ga sahihancin zaben shugaban kasar.

A ranar Alhamis ne ministan harkokin wajen Iran ya aike da sammaci ga jakadan Switzerland dake kasar, wanda kuma ke zaman wakilin Amurka a Iran, domin adawa da ikirarin da ake cewa, Iran na katsalandan cikin harkokin zaben Amurka. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China