2020-10-21 13:46:36 cri |
Wani bincike da kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Civil Liberlities Union(ACLU) ta bayyana Talatar nan cewa, lauyoyin da babban jojin tarayyar Amurka ya nada, sun bayyana cewa, har yanzu ba su gano iyayen yara 545 da aka raba da iyalansu a kan iyakar Amurka da kasar Mexico tsakanin shekarar 2017 da 2018 ba.
Kafar watsa labaran NBS ta bayyana cewa, lokacin da gwamnatin Trump ta bijiro da wannan manufa ta raba yara da iyaye bakin haure a kan iyakar kudancin kasar, ya fara raba iyalai ne a shekarar 2017 a wani bangare na kan iyakar kasar dake karkashin wannan shiri.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China