2020-10-04 21:15:38 cri |
Sunan zane-zanen da ta yi Xiang Xiang, inda suka nuna yadda wata ma'aikaciyar jinya 'yar Panda take aiki da zaman yau da kullum da sauran wasu labarai masu ban sha'awa.
A da Iwasaki Haruka ta yi shirin kammala aikinta na sa-kai a Beijing a watan Yulin bana, amma saboda aukuwar cutar COVID-19, ta dawo kasar Japan a karshen watan Janairu. Bayan da ta koma kasarta, har kullum ta kan maida hankali kan yadda kasar Sin take yaki da cutar.
Iwasaki Haruka ta kuma kara wasu abubuwa a cikin zane-zanen da ta wallafa, wato 'yar Panda Xiang Xiang ta fara fadakar da al'umma kan ilimin da ya shafi kandagarkin cutar COVID-19, ciki har da sanya abun rufe baki da hanci, da wanke hannu da sauransu. Kana, Xiang Xiang ta kan karfafa gwiwa ga ma'aikatan jinyar kasar Sin. Wadannan zane-zanen sun samu karbuwa sosai a shafin sada zumunta, inda mutanen kasar Sin da dama suka godewa Iwasaki Haruka, saboda goyon-bayanta musamman a matsayin wata bakuwa 'yar kasar waje.(Murtala Zhang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China