Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin cututtukan Rasha: Ba za a samu bullar COVID-19 karo na biyu a Sin ba
2020-10-13 19:15:49        cri

Rahotanni na nuna cewa, yanzu adadin masu kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Sin bai zarce sama da dubu 85 ba, yayin da har yanzu wasu kasashe a sassa na duniya ke fama da wannan annoba.

Kan wannan batu ne masanin cututtuka na kasar Rasha Anatoly Altstein, ya bayyana cewa, ba za a samu bullar cutar karo na biyu a kasar Sin ba. Dalilin kuwa shi ne, yadda mahukuntan kasar ta Sin suka dauki managartan matakan dakile yaduwar cutar gami da yadda jama'a suke nuna da'a da sadaukar da kai kan matakan da aka tsara na yaki da cutar.

Ya ce, kasar Sin ta ga bayan wannan annoba, amma wasu kasashe ba ma kawai sun gaza dakile yaduwar cutar tun a matakin farko ba, har ma sun gaza daukar matakan da suka dace na ganin bayan cutar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China