Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jamiin IMF ya ce aiwatar da muhimman sauye-sauye za su taimakawa kasar Sin wajen samun farfadowa bisa hanyoyi biyu
2020-11-05 11:26:17        cri

Wani jami'in asusun bada lamunin na IMF ya ce, ci gaba da aiwatar da muhimman sauye-sauye za su taimakawa kasar Sin wajen samun cikakkiyar farfadowa daga annobar numfashi ta COVID-19 da kuma sabon tsarin kasar na bunkasa ci gaban tattalin arzikinta bisa matakai biyu.

Na farko an bullo da shi a watan Mayun wannan shekara, mai take "dual circulation" wato wani tsari ne wanda ke dora muhimmanci ga kasuwanni cikin gida a matsayin jigo, yayin da kuma yake bada dama ga kasuwannin ketare ikon yin gogayya da juna, wannan batu ya samu fifiko matuka daga hukumomin kasar Sin bisa la'akari da yadda tattalin arzikin duniya ya gamu da babbar illa daga annobar COVID-19.

Shirin dogon zango, wadannan sauye-sauye za su kara bunkasa cigaba a cikin gida, kana za su taimaka wajen kara samun bunkasuwa, da kyautatuwa, da bunkasuwar tattalin arzikin dukkan fannoni, wanda ya yi daidai da sabuwar ajandar raya cigaba na hukumomin kasar.

A lokaci guda kuma, ya kamata kasar Sin ta cigaba da taimakawa wajen jagorantar tsarin gamayyar bangarori daban daban domin tinkarar manyan kalubalolin duniya, a cewar Berger, inda ya buga misali game da tallafawa yunkurin kasa da kasa wajen fadada shirin samar da rigakafi, da tsarin saukaka bashi ga kasashe masu karancin kudaden shiga, da zuba jari a fannin bunkasa samar da kayayyakin more rayuwa na kasa da kasa, da kuma warware matsalar sauyin yanayi. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China