2020-07-17 14:15:28 cri |
Manajar daraktar asusun bada lamini na kasa da kasa IMF Kristalina Georgieva, ta bayyana cikin wani sharhi da aka wallafa a ranar Alhamis cewa, ya kamata kasa da kasa su karfafa hadin gwiwa a fannoni da dama, wanda hakan yana da matukar muhimmanci wajen takaita tsawon lokacin da za'a dauka kafin farfadowa daga annobar COVID-19 a fadin duniya.
Cikin rahoton da asusun na IMF ya fitar a wannan rana ya nuna cewa, tattalin arzikin duniya yana farfadowa daga mawuyacin halin da ya fada, amma har yanzu akwai rashin tabbas game da makomar tattalin arzikin duniyar. (Ahmad)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China