Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sabuwar shawara game da tsarin raya kasar Sin ta nuna burin al'ummar kasar
2020-10-30 13:47:57        cri
Daga ranar 26 zuwa 29 ga watan da muke ciki, an gudanar da cikakken zama na 5 na kwamitin tsakiya na 19 na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda manyan kusoshin jam'iyyar dake rike da ragamar mulkin kasar sun tantance, gami da zartas da wata shawara game da shirin raya kasa na shekaru 5 masu zuwa, da babban burin raya kasar nan da shekarar 2035. Dangane da wannan taro, kwamitin tsakiya na JKS ya kira taronsa na manema labaru na farko a yau Juma'a, inda mataimakin darektan sashin watsa labarai na kwamitin tsakiya na JKS, mista Wang Xiaohui, ya ce, shawarar da aka zartas a wannan karo, ta nuna wani sabon salo na zamani, da sabbin bukatun da ke akwai, gami da sabbin burikan da jama'ar kasar suka sanya a gaba, wadda za ta ba da jagoranci ga aikin raya tattalin arziki da jin dadin al'ummar kasar Sin cikin shekaru 5 da kuma wasu dimbin shekaru masu zuwa.

Jami'in ya jaddada cewa, cikin shawarar an tabbatar da wani babban burin da aka sanya a gaba, na gina kasa ta zamani dake bin tsarin siyasa na gurguzu, daga dukkan fannoni, inda za a mai da hankali kan neman samun ci gaba mai inganci, da zurfafa gyare-gyare a bangaren samar da kayayyaki, da aikin kimiyya da fasaha, da kirkiro sabbin fasahohi, da habaka bukatu a kasuwannin cikin gida, da tabbatar da samun ci gaba da tsaron kasa.

A cikin shawarar da aka gabatar, a karon farko an sanya burin samun cikakken ci gaba a kokarin tabbatar da wadatar da daukacin al'umma. Kana an tsara wasu manyan ayyukan da za a mayar da hankali a kansu, yayin da ake dora muhimmanci kan kasuwannin cikin gida, gami da kokarin tabbatar da cudanyar kasuwannin cikin gida da na kasashen waje. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China