Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ce ke kan gaba a tsayin layukan dogo a duniya
2020-10-29 11:01:27        cri

Wasu alkaluman baya bayan nan da aka fitar sun nuna cewa, kasar Sin ce ke kan gaba a duniya, wajen tsayin layukan dogo, yayin da aikin ginin layukan dogon kasar ya kara fadada, karkashin tsarin raya kasa na shekaru 5 karo na 13 da kasar ke aiwatarwa tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020.

Rahotanni na cewa, ana hasashen fara aiki da karin layukan dogo da tsayin su ya kai kilomita 146,000 ya zuwa karshe wa'adin tsarin raya kasa na shekaru 5 karo na 13, wadanda za su karade kaso 99 bisa dari na biranen kasar, masu kunshe da yawan al'ummu sama da 200,000.

Kaza lika an bayyana cewa, cikin wadannan layukan dogo, akwai masu saurin tafiya da tsayin su ya kai kusan kilomita 38,000, wadanda kuma suka zamo mafi tsayi a duk duniya, sun kuma haura na sauran kasashen duniya idan an hada su baki daya.

A yayin da hanyoyin layukan dogo na kasar Sin ke karade sassan birane, tsayin hanyoyin motar kasar sun kai kilomita miliyan 5.1. Tsakanin shekarar 2016 zuwa 2019, an kuma gina titunan mota masu tsawon kilomita 96,000 a yankunan karkara masu yawan jama'a matalauta. Kaza lika kauyukan kasar 556,000 na da hanyoyin aikewa da sakwanni na zamani da al'ummun su ke amfani da su. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China