Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Faransa ta daga matsayin matakan tsaron cikin gida
2020-10-30 15:07:50        cri
Mahukunta a kasar Faransa, sun bayyana daukar karin matakan tsaro, bayan da wani mutum ya dabawa wasu mutane dake cikin wata majami'a wuka a ranar Alhamis.

Yayin wani taron manema labarai da ya gudana, mai gabatar da kara na sashen yaki da ayyukan ta'addanci a Faransa Jean-Francois Ricard, ya ce maharin dan asalin kasar Tunusia ne, ya kuma shiga Faransa daga Italiya a farkon watan Oktoba.

Mr. Ricard ta kara da cewa, maharin ya kutsa kai majami'ar Notre-Dame dake tsakiyar birnin Nice ne da sanyin safiyar jiya Alhamis, kuma nan take ya rika dabawa mutanen dake cikin majami'ar wuka, lamarin da ya sabbaba kisan mutane a kalla 3, da jikkatar wasu da dama, kafin daga bisani 'yan sanda su harbe shi.

Rahotanni sun ce bayan harbin da 'yan sanda suka yiwa maharin an garzaya da shi asibiti, inda yake cikin yanayi na mutu kokwai rai kokwai.

Shugaban kasar Emmanuel Macron, wanda ya gabatar da jawabi daga inda harin ya auku, yayi Allah wadai da harin da ya ce na ta'adanci ne, yana mai shan alwashin daukar matakan dakile dukkanin wata barazana ta aikata ta'adanci a kasarsa.

Shugaban na Faransa ya kara da cewa, bayan harin na jiya, an daga matsayin matakan tsaron kasa zuwa mataki na karshe, inda aka shirya jibge karin dakarun tsaro 4,000 a sassan kasar daban daban, ciki har da wuraren bauta da makarantu. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China