2020-08-30 16:56:36 cri |
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, wanda ke ziyarar aiki a kasar Faransa ya bayana cewa, kasashen Sin da Faransa, muhimman kasashe ne dake da muhimmin nauyi a bisa wuyansu wajen bunkasa tsarin gamayyar bangarori daban daban wanda yake da matukar alfanu ga moriyar mafi yawan kasashen duniya, musamman kanana da matsakaitan kasashen duniya.
A tattaunawar da ya yi da takwaransa na Faransa Jean-Yves Le Drian, Wang Yi ya gabatar da shawawari guda hudu ga kasashen biyu.
Da farko, kasashen Sin da Faransa suna bukatar bin manufar tsarin hadin gwiwar bangarori daban daban. Ya kamata bangarorin biyu su yi kokarin kara azama kan tsarin gamayyar bangarori daban daban a matakai daban daban, su yi adawa da ra'ayi na kashin kai kuma su yi kokarin mayar da tsarin gamayyar bangarori daban daban a matsayin wani tsarin da kasa da kasa da suka amince da shi.
Na biyu, ya kamata a aiwatar da tsarin hadin gwiwar bangarori daban daban. Kasar Sin tana goyon bayan Faransa wajen ci gaba da taka muhimmiyar rawa don daidaita batun sauyin yanayi. Kasar Sin ta riga ta cimma manufarta ta rage fitar da iska mai dumamar yanayi a shekarar 2020 tun gabanin cikar wa'adin da aka kebe, kuma tana nazarin dorawa zuwa mataki na gaba. Ya kamata kasashen biyu su tallafawa juna wajen shirya babban taron kasashen da suka daddale yarjejeniyar kiyaye kasancewar mabambantan halittu a duniya a birnin Kunming na kasar Sin dake tafe, da kuma taron kasa da kasa kan kiyaye halittu da za a gudanar a birnin Marseille na kasar Faransa, dukkan tarukan za a gudanar da su ne a shekara mai zuwa.
Na uku, ya kamata kasashen Sin da Faransa su mutunta yarjejeniyoyin hadin gwiwar bangarori daban daban. Nuna ra'ayin bangare daya, wanda ya kunshi nuna rashin dattaku na janyewa daga kungiyoyin kasa da kasa ko kuma saba yarjejeniyoyin kasa da kasa, ba abu ne dake samun karbuwa ba. Ya kamata Sin da Faransa su karfafa hadin gwiwarsu kan al'amurran kasa da kasa, kuma su yi kokarin kiyaye muhimman sakamakon da aka fitar na yarjejeniyoyin kasa da kasa da tsarin diflomasiyyar gamayyar kasa da kasa, kamar batun yarjejeniyar nukiliyar Iran.
Na hudu, ya kamata a karfafa hukumomin hadin gwiwar bangarori daban daban. MDD ita ce hukuma mafi muhimmanci da take tallafawa tsarin hadin gwiwar bangarori daban daban da aiwatar da shi a zahiri, ya kamata kasashen biyu su goyi bayan MDD a kokarinta na sauke nauyin dake bisa wuyanta a harkokin kasa da kasa. (Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China