Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsara shirin shekaru biyar-biyar karo na 14 ya shaida tsarin demokuradiyya mai tsarin gurguzu ta kasar Sin
2020-10-30 13:46:03        cri
An rufe taron cikakken zama na biyar na kwamitin koli na JKS na 19, inda aka amince da shawarwarin da kwamitin koli na JKS ya gabatar, game da shirin raya tattalin arziki da jin dadin jama'a na shekaru biyar-biyar karo na 14, da manufofin da ake fatan cimmawa na dogon lokaci zuwa shekarar 2035. A yayin taron manema labaru na farko da kwamitin tsakiya na JKS ya gudanar a yau, mataimakin shugaban ofishin kwamitin kudi na kwamitin tsakiya na JKS Han Wenxiu ya bayyana cewa, tsara shirin shekaru biyar-biyar karo na 14 ya shaida tsarin demokuradiyya mai sigar gurguzu ta kasar Sin.

Ya ce, shugaba Xi Jinping ya ba da umurnin cewa, ya kamata a hada aikin tsara shirye-shirye da ra'ayoyin jama'a tare, da sa kaimi ga jama'ar kasar da su bada shawarwari ta hanyoyi daban daban. Tun daga ranar 16 zuwa 29 ga watan Agusta, an nemi ra'ayoyi ta yanar gizo kan yadda za a tsara shirin shekaru biyar-biyar karo na 14. Jama'ar kasar sun ba da ra'ayoyi da dama, inda yawan ra'ayoyin da aka tattara ta yanar gizo ya kai fiye da miliyan daya, kana hukumomin da abin ya shafa sun nemi ra'ayoyi da shawarwari fiye da dubu daya.

Game da tsarin shirin shekaru biyar-biyar karo na 14, Han Wenxiu ya yi nuni da cewa, muhimman abubuwan da aka shaida a cikin tsarin shi ne sabbin fannoni uku, wato sabon matakin samun bunkasuwa, da sabon tunanin samun bunkasuwa, da kuma sabon tsarin samun bunkasuwa.

Sa'an nan game da manufar bude kofa ga kasashen waje da kasar Sin ke gudanarwa, Mista Han ya ce sabon tsarin raya kasa da ake fatan aiwatarwa a kasar Sin, ya jaddada muhimmancin cudanyar kasuwannin cikin gida da na kasashen waje, gami da kara bude kofar kasar ga kasashen waje. Kana za a samar da karin damammaki ga kamfanonin kasashen waje domin su shiga cikin kasuwannin kasar Sin, ta hanyar samar da wani yanayi mai kyau, da sanya kasar Sin ta zama mai janyo ingantattun albarkatun kasa da kasa, da wurin da 'yan kasuwan kasashen waje za su yi sha'awar zuba jari da raya sana'o'insu, don cimma burin tabbatar da moriya da wadatar kasashe daban daban. (Zainab/Bello)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China