Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin kolin JKS na 19 zai gudanar da zama na 5 a watan Oktoba
2020-07-30 21:11:18        cri
Hukumar siyasa ta kwamitin koli na JKS ta sanar da cewa, kwamitin kolin JKS na 19 zai gudanar da zamansa na 5 a watan Oktoba mai zuwa. Ofishin hukumar siyasar ya bayyana amincewa da hakan ne, yayin zaman sa na yau Alhamis. Shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, shi ne ya jagoranci taron na yau.

Kaza lika a yayin taron na yau, hukumar siyasa na kwamitin koli na JKS, ya duba halin da tattalin arzikin Sin ke ciki, tare da tsara aikin da za a gudanar a watanni 6 na karshen shekarar.

Ana sa ran yayin taron na watan Oktoba, hukumar siyasa ta kwamitin koli na JKS, za ta gabatar da rahoton aikin sa, lokacin da kuma mahalarta taron za su nazarci shawarwari da aka gabatar, game da tsarin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin na shekaru biyar biyar na 14, wanda za a aiwatar tsakanin shekarun 2021 zuwa 2025, da ma kudurin ci gaban kasar, na nan da shekarar 2035. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China