Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An fitar da sanarwar bayan taron cikakken zama na biyar na kwamitin kolin JKS na 19
2020-10-29 20:38:55        cri

A yau ne aka fitar da sanarwar bayan taron cikakken zama na biyar na kwamitin koli na JKS na 19, wanda ya gudana daga ranar 26 zuwa 29 ga watan Oktoban wannan shekara a nan birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin.

Xi Jinping, babban sakataren kwamitin koli na JKS, ya gabatar da muhimmin jawabi yayin wannan zama, inda aka saurara tare da tattauna rahoton aiki da ya gabatar a madadin hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS.

Haka kuma a yayin wannan zama, an amince da shawarwarin da kwamitin koli na JKS ya gabatar game da shirin raya tattalin arziki da jin dadin jama'a na shekaru biyar-biyar karo na 14, shirin da za a aiwatar daga shekarar 2021 zuwa ta 2025, da manufofin da ake fatan cimma na dogon lokaci zuwa shekarar 2035.

Sanarwar bayan taron da aka fitar,  ya bayyana cewa, shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 13 da aka aiwatar daga shekarar 2016 zuwa ta 2020, ya haifar da bunkasar tattalin arziki da fasahohin kasar kana karfin kasar ya kai wani sabon matsayi, baya ga yadda tsarin tattalin arzikin kasar ke ci gaba da inganta.

Bugu da kari, sanarwar ta ce, kasar Sin za ta zurfafa gyare-gyare a kokarin da take na zama babbar kasuwa mai sigar gurguzu, tare da kara bude kofarta ga kasashen ketare don bullo da sabbin damammaki na hadin gwiwa da juna.

Kasar Sin za ta nace ga aiwatar da kirkire-kirkire, a kokarin da take na samun ci gaban zamani, da kara inganta rayuwar al'ummarta. Sanarwar ta kara da cewa, kasar Sin za ta yi kokarin tabbatar da samun bunkasuwa da tsaron kasa da ci gaba da aiwatar da manufar kasar ta samun ci gaba cikin lumana.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China