Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadarin mota ya hallaka yara 'yan makaranta 21 Enugu
2020-10-30 09:37:55        cri
Kwamandan hukumar kare hadurra ta tarayyar Najeriya FRSC,reshen jihar Enugu dake kudu maso gabashin kasar Ogbonnaya Kalu, ya tabbatar da rasuwar a kalla yara 'yan makaranta su 21, sakamakon hadarin mota da ya rutsa da su ranar Laraba, a hanyar Enugu zuwa Okigwe dake kudancin jihar.

Mr. Kalu ya ce baya ga yaran da suka rasu, akwai kuma wasu da dama da suka jikkata cikin motar da ke makare da mutane. Jami'in ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, wata babbar mota ce ta kwace wa direbanta, ta kuma yi karo da Bas din da suke ciki. Ya kuma kara da cewa, Bas din dake dauke da yaran na da fasinjoji 64, ciki har da malaman su, a lokacin da hadarin ya auku.

Shaidun gani da ido sun ce an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti, yayin da direban babbar motar da ta haddasa hadarin ya tsere. Tuni kuma 'yan sanda suka fara bincike game da aukuwar hadarin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China