Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na kara jawo jarin waje
2020-10-28 21:11:03        cri
Rahoton da taron MDD kan kasuwanci da bunkasuwa ko kuma UNCTAD a takaice ya bayar ya nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Satumbar bana, yawan jarin wajen da aka zuba a kasar Sin ya karu sosai. Game da hakan, mai magana da yawun ma'aikata harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana cewa, karuwar ta shaida cewa kasashen duniya suna da yakini sosai kan makomar bunkasuwar Sin, kana, nasara ce da kasar ta samu a fannin ci gaba da aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje.

Rahoton ya ce, daga watan Janairu zuwa Yunin bana, yawan jarin ketare da aka zuba kai-tsaye a kasashen duniya wato FDI a takaice ya ragu da kaso 49 bisa dari, yayin da jarin wajen da suka shigo kasar Sin, ya ci gaba da karuwa. Har wa yau, ya zuwa watan Satumbar bana, yawan karuwar jarin wajen da Sin ta jawo kai-tsaye ya karu da kaso 2.5 idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China