Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta fitar da ka'idojin kyautata yanayin kasuwanci ga baki masu zuba jari
2019-10-30 10:17:33        cri
Kasar Sin za ta gabatar da ka'idojin na kyautata amfani da jarin baki bisa mayar da hankali kan kiyaye yadda kasar ke tafiyar da kamfanonin bakin.

Mataimakin ministan cinikayya, kuma mataimakin wakilin kasar Sin kan harkokin cinikayyar kasa da kasa, Wang Shouwen ya ce ka'idojin da aka amince da su yayin taron majalisar gudanarwar kasar Sin na ranar 16 ga wata, ya kunshi manufofi 20 a fannoni 4, wadanda ke da nufin samar da sahihin yanayin kasuwanci ga kamfanonin baki.

Da farko, ta fuskar fadada bude kofa, kasar Sin za ta ci gaba da rage jerin bangarorin da baki ba za su iya zuba jari ba a kasar da kuma yankuna cinikayya mara shinge na gwaji, da kuma kawar da sauran tarnakin da ba sa cikin wadancan jerin bangarori. Sannan kasar Sin za ta gaggauta bude kofa a bangaren hada-hadar kudi da kyautata manufofin zuba jarin waje a bangaren ababen hawa.

Na biyu, a fannin inganta zuba jari, kasar Sin za ta kyautata ayyukan kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha ga kamfanonin baki, da kuma inganta ginin yankunan cinikayya na gwaji.

Na uku, a fannin zurfafa gyare-gyare a gida da saukaka zuba jari, kasar sin za ta rage kudaden da aka shigo da su daga kasashen ketare da saukaka aiki a kasar Sin ga baki da inganta tsarin amincewa da amfani da fili domin gudanar da ayyukan da baki suka samar da kudin aiwatar da su.

Na hudu kuma, a bangaren kare hakkin mallakar fasaha da muradun baki masu zuba jari, Sin za ta zartar da dokokin zuba jari na baki da kafawa tare da inganta cibiyoyin karbar korafe-korafe. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China