Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin zata janyo hankalin masu zuba jari daga waje ta hanyar kyautata muhallin kasuwanci
2019-10-17 10:23:28        cri
Kasar Sin zata bullo da sabbin matakan kara inganta muhallin kasuwanci da nufin janyo hankalin masu zuba jari daga kasashen ketare, majalisar gudanarwar kasar ce ta sanar da hakan a lokacin taron majalisar na ranar Laraba wanda firaiminista Li Keqiang ya jagoranta.

Taron ya yanke shawarar bude kofa a karin wasu bangarorin. Da soke wasu tsauraran matakai da ba su cikin jerin fannonin da aka hana saka jarin waje a fadin kasar da ma bangaren yankunan ciniki na gwaji.

Za a kuma janye matakan da suka kayyade wasu ayyukan da bankuna da kamfanonin samar da takardun hada-hadar kudi masu jarin waje ke gudanarwa a kasar.

Li ya ce, "tilas ne mu inganta manufofinmu kuma mu aiwatar dasu yadda ya kamata,". "Dole mu kiyaye alkawurran da muka dauka. Ba zamu taba saba maganganunmu ba."

Wasu alkaluma da ma'aikatar cinikin kasar Sin ta fitar a watan Satumba ya nuna cewa, a watannin takwas na farkon wannan shekarar, kimanin masu zuba jarin waje 27,704 ne suka kafa kamfanoninsu a kasar Sin. Kudaden da suke hada hadarsu ya zarta yuan biliyan 600 kwatankwacin dala biliyan 84.81, wanda ya karu da kashi 6.9 na makamancin lokacin bara.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China