Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Faransa za ta mika wanda ake zargi da hannu a kisan kiyashin Ruwanda ga kotun Hague
2020-10-28 13:55:39        cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Faransa, ta bayar da sanarwa a jiya cewa, Faransan ta mika Félicien Kabuga, mutumin da aka zarga da hannu a kisan kiyashin kasar Ruwanda ga kotun Hague dake kasar Netherland.

Félicien Kabuga mai shekaru 84 da haihuwa, ya taba yin harkokin cinikayya a kasar Ruwanda. A shekarun baya baya nan, ya yi amfani da takardar shaidar asali ta jabu don ci gaba da rayuwa a kasar Faransa.

A yayin kisan kiyashi na Ruwanda, Kabuga ya tada zaune tsaye ta kafar rediyonsa, da kuma samar da kudi don goyon bayan kisan kiyashin. A watan Mayu na bana ne kuma, aka kama shi a karkarar birnin Paris na kasar Faransa. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China