Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Adadin masu dauke da COVID-19 a duniya ya zarce miliyan 30
2020-09-19 16:52:48        cri

Alkaluman baya bayan nan da hukumar lafiyar ta duniya WHO ta fitar ya nuna cewa, adadin mutanen da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a fadin duniya ya zarce miliyan 30.

A duniyar baki daya, ya zuwa karfe 16:01 agogon tsakiyar Turai wato karfe 14:01 agogon GMT, na ranar Juma'a, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 ya kai 30,055,710, wanda ya hada har da mutane 943,433 da cutar ta kashe, kamar yadda rahoton hukumar WHO ya bayyana.

Amurka ce kasar dake sahun gaba a yawan mutanen da suka kamu da kuma mutanen da cutar ta kashe, inda mutane 6,571,119 ne aka tabbatar sun harbu da cutar, sai mutane 195,638 da annobar ta hallaka a kasar. Sai kasashen Indiya da Brazil dake bi mata baya, a kasar Indiya, an tabbatar da mutane 5,214,677 sun kamu da cutar yayin mutane 84,372 cutar ta hallaka, an tabbatar da mutane 4,419,083 sun kamu da cutar a Brazil, kana cutar ta kashe mutane 134,106 a kasar , in ji hukumar ta WHO.

Babban daraktan hukumar WHO Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yi gargadi yayin taron manema labaru a ranar Juma'a cewa, annobar COVID-19 ta nunawa duniya cewa baki daya, duniyar ba a shirye take ba.

Ya ce, hanya daya tilo da za a iya tinkarar wannan mummunar barazanar dake addabar duniya ita ce, duniya ta kasance tsintsiya madaurinki daya.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China