Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: COVID-19 ta haifar da manyan sauye-sauye ga babban taron shekara-shekara na MDD
2020-09-09 09:23:15        cri

Stephen Dujarric, mai magana da yawun babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana cewa, dokokin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 da aka sanyawa bakin da za su halarci babban taron shekara-shekara na MDD, da zai hallara shugabannin kasashen duniya da za a gudanar a wani lokaci a wannan wata, zai sha bamban da tarukan baya.

Dujarric wanda ya bayyana haka, yayin taron manema labarai ta kafar bidiyo, ya ce yayin taron karo na 75, za a ji abin da shugabannin za su fada game da halin da duniya take ciki a wannan lokaci mai sarkakiya da muke rayuwa, yana kuma tunanin, ya dace a canja halin da ake ciki, ta yadda al'amura za su koma kamar yadda suke a baya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China