Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya fi kyau Amurka ta warware matsalolinta a maimakon yin karya
2020-10-20 19:57:11        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yau Talata a nan birnin Beijing cewa, kasar Amurka ba ta da kyakkyawan tarihi na kiyaye hakkin dan Adam, da tabbatar da 'yancin kai ta fuskar addini a cikin gida. Jami'in ya ce kamata ya yi, ta mai da hankali kan warware matsalolinta, a maimakon yiwa sauran kasashe karya.

Kwanan baya, ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ta wallafa a shafinta na yanar gizo cewa, sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo, ya ba da wata sanarwa, dangane da sa ido da yaki da fataucin mutane, inda ya sossoki matakan da kasar Sin ke dauka a jihar Xinjiang, da batun addini. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China