Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Guterres ya yi kira da a tafiyar da harkokin kasa da kasa bayan COVID-19 ta hanyar sadaukar da kai da cudanyar bangarori daban-daban
2020-09-25 15:12:15        cri
Babban sakataren MDD, Antonio Guterres ya yi kira da a tafiyar da harkokin kasa da kasa bayan annobar COVID-19, bisa shigar sadaukar da kai da cudanyar bangarori daban-daban.

Guterres wanda ya bayyana haka, yayin babban taron muhawarar da aka shirya, kan tafiyar da harkokin kasa da kasa bayan annobar COVID-19, ya ce, annobar ta sake bayyana karin manyan kalubale da ka iya kunno kai, farawa da matsalar sauyin yanayi. A don haka, idan muka tunkari wadannan matsaloli ta hanyar rashin nuna hadin kai da yarda da juna, mun ga abin da ya faru a wannan shekara, kuma "Ina fargabar abin da zai iya biyo baya".

A don haka, jami'in na MDD ya ce akwai bukatar tafiyar da harkokin kasa da kasa mai nagarta, da sauki, tsarin da zai tunkari duk wani kalubale da muke fuskanta.

Ya kara da cewa, COVID-19, gargadi ne da wajibi duniya ta dauki mataki a kai. Ya ce, "ba mu da zabi, ko dai mu kasance tsintsiya madaurinki daya, da za ta iya tunkarar duk wata matsala, ko kuma rarrabuwar kawu na da rikice-rikice za su raba kanmu.

Ya kuma lura da cewa, kokarin samar da alluran riga kafin annobar tare, zai rage yawan mace-mace ta hanyar kula da ma'aikatan lafiya gami da mafiya rauni, baya ga kokarin da duniya ta ke yi na samar da kudaden da ake bukata, don ganin al'ummar duniya ta ci gajiyar riga kafin, isassu da kowa zai iya samu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China