Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu kungiyoyin Afrika sun sha alwashin kare hakkin mata, matasa, da kananan yara a nahiyar
2019-08-25 16:20:55        cri
Shugaban kungiyar matasan Libya NOLY, Khaled Ghouil, ya bayyana a birnin Tunis cewa, sun bullo da wani shirin hadin gwiwa na kasashen Afrika wanda zai taimaka wajen kare hakkin mata, kananan yara, da matasa a nahiyar.

A lokacin wani taron karawa juna sani wanda kungiyar matan Tunisiya UNFT, ta shirya tare da hadin gwiwar kungiyar NOLY, da kungiyar tuntuba ta matan kasar Tunisiya, da kungiyar dalibai da matasan yankin Sahel da kasashen yankin hamadar Sahara, da kuma majalisar matasan Tunisiya, Ghouil yace, kungiyoyin sun sha alwashin yin aiki tukuru wajen lalibo hanyoyin warware dukkan matsaloli da kalubalolin dake damun mata da matasan Afrika.

A cewar shugaban na NOLY, wannan shirin an bullo dashi ne da nufin hada kan dukkan kungiyoyin mata da matasa na kasashen Afrika.

A nata bangaren, shugabar UNFT Radhia Jeribi tace, shirin zai yi cikakken nazari wajen binciko dukkan muhimman hanyoyin da zasu warware matsalolin dake damun mata da matasan Afrika, kamar matsalar talauci, jahilci, cin rani, yake yake, da rikicin siyasa.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China