Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nahiyar Afrika ta yi alkawarin kara karfafawa mata gwiwa
2020-02-17 10:26:30        cri
Tarayyar Afrika AU ta bayyana kudurinta na kokarin tallafawa matan nahiyar, ta yadda za su ci gajiyar yarjejeniyar kafa yankin ciniki cikin 'yanci na Afrika, da aka fara amfani da ita a nahiyar.

Domin kara aiwatar da matakan da za su inganta tafiya da dukkanin jinsi wajen samun ci gaba mai dorewa, shugabannin nahiyar sun ayyana shekarun 2020 zuwa 2030, a matsayin karnin shigar da mata cikin aikin raya harkokin kudi da na tattalin arziki.

Cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar, tarayyar mai kasashe mambobi 55, ta jaddada kudurinta na kokarin ingiza wannan shiri, yayin da mata da 'yan mata ke neman karin damarmaki, musammam wajen aiwatar da yarjejeniyar yankin ciniki cikin 'yanci.

AU ta yi alkawarin yarjejeniyar za ta amfanawa mata dake kasuwanci tare da ba su damar ba da tasu gudunmuwa, domin inganta yanayin mata 'yan kasuwa a fadin nahiyar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China