Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi da takwaransa na Equatorial Guinea sun taya juna murnar cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu
2020-10-15 11:09:10        cri
Yau Alhamis, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da ministan harkokin wajen Equatorial Guinea Simeon Oyono Esono Angue, sun taya juna murnar cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu, ta wayar tarho.

Wang Yi ya ce, Sin da Equatorial Guinea 'yan uwan juna ne, bayan da aka kulla huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu, cikin wadannan shekaru 50 da suka gabata, kasashen biyu sun raya dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata, da kuma zurfafa fahimtar juna ta fuskar siyasa a tsakaninsu. Haka kuma, an cimma sakamako da dama bisa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, suna goyon bayan juna a harkokin kasa da kasa da kuma yin hadin gwiwa yadda ya kamata wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19. Wang Yi ya kara da cewa, yana son karfafa hadin gwiwa da mista Simeon Oyono Esono Angue, domin aiwatar da matsaya guda da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da sakamakon da aka cimma a taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka na birnin Beijing, da kuma sakamakon da aka cimma a taron kolin yaki da cutar COVID-19 cikin hadin gwiwa, ta yadda za a inganta dangantakar abokantaka a tsakanin Sin da Equatorial Guinea bisa dukkan fannoni.

A nasa bangaren, Simeon Oyono Esono Angue ya ce, bayan da aka kulla huldar diflomasiyya a tsakanin Sin da kasarsa, kasashen biyu sun yi hadin gwiwa mai kyau a fannoni da dama, lamarin da ya taimakawa kasar Equatorial Guinea wajen kyautata ababen more rayuwa da zaman al'umma, hakan ya zama abin misali wajen yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe maso tasowa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China