Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Ma'anar babbar kasa ita ce sauke nauyi mafi girma
2020-09-28 11:20:39        cri

A jiya Lahadi, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya zanta da shugaban babban taron MDD karo na 75 Volkan Bozkır ta wayar tarho. Yayin zantawar tasu, Wang ya yi nuni da cewa, kamata ya yi kasashe daban-daban, su kara hadin kansu, duba da yadda cutar COVID-19 ke ci gaba da addabar duniya, ta yadda za a tinkari wannan mummunar cutar tare.

Wang Yi ya kara da cewa, Sin na goyon bayan MDD bisa rawar da take takawa a wannan fanni, tana kuma fatan ci gaba da hadin gwiwa da sassan daban-daban na majalisar, wajen kin amincewa da siyasantar da batun cutar, da ma dora laifi kan wata kasa game da cutar, ta yadda za a bi hanya mafi dacewa don hadin kan kasa da kasa wajen yakar cutar.

Wang ya kuma jaddada cewa, an shiga wani zamani na tuntubar juna, hakan ya sa ra'ayin bangaranci, da manufar ba da kariya, da manufar wariya ba za a yarda da su ba. Ya ce duk wata babbar kasa ba za ta samu karin iko ba, sai ta sauke babban nauyin dake wuyanta mafi yawa.

Ya ce a matsayin zaunanniyar mamba a kwamitin sulhun MDD, Sin za ta nace ga goyon bayan tsarin kasa da kasa karkashin jagorancin MDD, da ma marawa zaman doka da odar duniya baya, bisa tushen dokar kasa da kasa.

A nasa bangare, Volkan Bozkır ya ce, a matsayinsa na shugaban taron, aikin da ya sa gaba a wannan karo shi ne, sa kaimi ga cimma muradun samun bunkasuwa mai dorewa na shekarar 2030, da kokarin kawar da talauci, da tallafawa kasashe da suke bukata, musamman ma kanana da matsakaitan kasashe. Ban da wannan kuma, inganta da kiyaye manufar gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban, muhimmin aiki ne dake gaban taron. Kaza lika Sin sahihiyar abokiya ce a fannin gudanar da wannan manufa, yana kuma mai fatan kara hadin kai da ita. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China