Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya yi kira da a yi zabi na gari bayan kawar da COVID-19
2020-09-29 09:54:40        cri

Dan majalissar gudanarwa, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi kira ga daukacin kasashen duniya, da su yi zabi na gari domin inganta salon jagoranci, da aiwatar da dokokin kasa da kasa yadda ya kamata bayan kawar da cutar COVID-19.

Wang Yi wanda ya yi wannan tsokaci ne, yayin bude taron Lanting da ya gudana a birnin Beijing, ya ce duniya na cikin wani muhimmin lokaci tun bayan kawo karshen yakin duniya na II, inda har yanzu cutar COVID-19 ke addabar sassa daban daban, don haka salon daukar matsayar kashin kai, da nuna fin karfi na barazana ga tsarin gudanarwar duniya. A hannu guda kuma, kariyar cinikayya na yin tasiri ga tattalin arzikin duniya.

Wang Yi ya ce kamata ya yi daukacin sassan duniya su tambayi kan su inda suka dosa bayan kawo karshen COVID-19, tambayar da a cewar sa bai kamata a dauke ta da wasa ba.

Bugu da kari, Mr. Wang ya ce yayin babban taron MDD na 75, sassan kasa da kasa sun amince da matsayin MDD, kasancewar ta dandali mafi tasiri ga cudanyar kasa da kasa, kuma yanayin cudanyar dukkanin sassa ya kasance ginshikin tsarin kasa da kasa da ake bi a halin yanzu, yayin da goyon baya da hadin gwiwa suka zamo hanyoyi kadai na kawo karshen yaduwar cutar.

Ya ce kasashen duniya, manya da kanana, masu karfi da raunana, matsayin su guda ne a dandali na kasa da kasa. Kuma wadanda ke ganin suna da karfi da zai ba su ikon karya ka'idojojin kasa da kasa, za su rasa abokan tafiya a nan gaba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China