Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Jawabin Xi a babban taron MDD ya nuna abin da ke damun duniya da nauyin dake kan MDD
2020-10-02 16:46:07        cri
A yau ne mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya zanta da manema labarai, game da manyan tarukan da shugaban kasar Sin Xi jinping ya halartar yayin babban taron mahawarar MDD karo na 75.

Wang Yi, ya ce muhimmin jawabin da shugaba Xi ya gabatar, ya amsa manyan tambayoyi da duniya za ta fuskanta bayan annobar COVID-19, da irin rawar da kasar Sin za ta taka a duniya.

Ya ce, kasar Sin za ta nace kan tsarin cudanyar bangarori daban-daban, da kare ikon MDD, da bin turbar samun bunkasuwa cikin lumana, da hadin gwiwar moriyar juna, da yayata gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama.

Jawabin da shugaban Xi ya gabatar a babban taron na MDD, ya kuman bullo da sabbin dabarun hadin gwiwar kasa da kasa kan yaki da COVID-19, da matsaya daya da aka cimma na yiwa tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa gyaran fuska. Haka kuma, jawabin ya fito da wani sabon tsarin farfado da tattalin arzikin duniya, da gina tsarin muhallin duniya mai cike da wayewar kai. Bugu da kari jawabin ya kara taimakawa mata a duniya, ya kuma nuna sabon rawar da MDD za ta taka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China