Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda aka raya sana'ar shuka kayan lambu a jihar Tibet
2020-10-14 13:20:20        cri

An sha fama da karancin kayan lambu a jihar Tibet ta kasar Sin. A shekarar 1998, garin Bainang na birnin Rikaze ya shigar da fasahohin shuka kayan lambu na zamani daga lardin Shandong, domin habaka ayyukan shuka kayan lambu a yanki mai tudu. Ya zuwa yanzu, an kafa wani yankin samar da kayan lambu a garin Bainang, wanda ya zama abin misali a duk fadin kasar Sin.

A shekarar 2019, fadin gonakin shuka kayan lambu a jihar Tibet ya kai muraba'in kilomita 260, inda ta samar da kayan lambu ton dubu 970, lamarin da ya sa, dukkanin al'ummomin jihar suka samun kayan lambu wadanda ba su da tsada. An ce, cikin shekaru da dama da suka gabata, lafiyar jikunan al'ummomin jihar Tibet ta samu kyautatuwa sosai, sabo da kyautatuwar ayyukan jinya, da tsarin ba da hidima ga al'umma, da kuma kyautatuwar tsarin cin abinci bisa yadda suke samun kayan lambu da sauki.

Haka kuma, sana'ar shuka kayan lambu ta ba da gudummawar kawar da talauci a jihar Tibet. A garin Bainang, mutane sama da dubu 4 sun cimma nasarar kawar da talaucinsu, bisa bunkasuwar sana'o'in samar da kayan lambu da 'ya'yan itatuwa. A halin yanzu, cibiyoyin shuka kayan lambu na garin Bainang sun kasance abin misali a fannin raya fasahohin shuka kayan lambu a yanki mai tudu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China