Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana Dukufa Wajen Kare Muhallin Yankin Linzhi Na Jihar Tibet A Wani Mataki Na Neman Bunkasuwarsa
2020-09-30 13:34:37        cri

A 'yan shekarun nan, gwamnatin yankin Linzhi na jihar Tibet tana raya sana'o'i daban daban a yankin domin kawar da talauci, musamman ma a fannin kiwon aladan Zangxiang, wani irin alade na musamman da aka fitar a wannan yanki.

A shekarar 2018, kauyen Cuogao na yankin Linzhi ya zuba jarin Yuan miliyan 7.2, wajen kafa kwamitin hadin gwiwar masu kiwon aladan Zangxiang, domin magance wasu matsalolin yaduwar cututtuka tsakanin aladai, da kuma ba da taimako ga manoma, wajen fuskantar kalubaloli masu nasaba da hakan.

Sa'an nan, a shekarar 2018 kuma, an zuba jarin Yuan miliyan 92, a shirin kaurar al'ummomin kauyen Cuogao, domin kyautata yanayin zaman rayuwar su, da kuma kare gine-ginen gargajiya. Wadannan gine-ginen gargajiya da raye-rayen gargajiya na wurin, sun janyo hankulan masu yawon shakatawa kwarai da gaske, inda a shekarar 2010, aka shigar da raye-rayen cikin jerin harkokin al'adun gargajiya da aka gada daga kaka da kakkani na yankin Tibet.

Albarkacin al'adun gargajiya, sana'ar yawon shakatawa ta bunkasa matuka a kauyen Cuogao cikin 'yan shekarun baya bayan nan. Shugaban kungiyar raye-raye ta kauyen Cuogao ya ce, tabbas za a ci gaba da raya wannan raye-raye a nan gaba, za a kuma gayyaci karin baki don su yi yawon shakatawa a kauyensu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China