Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan nakasassu mata da suka fita daga kangin talauci karkashin taimakon gwamnatin kasar Sin ya kai miliyan 2.55 a karshen shekarar 2019
2020-09-29 10:59:05        cri

Kididdigar da kungiyar taimakawa nakasassu ta kasar Sin ta yi, ta nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar 2019, Sin ta taimakawa nakasassu mata kimanin miliyan 2.55 fita daga kangin talauci, matakin da ya kyautata zaman rayuwarsu.

An ce, ya zuwa karshen shekarar 2019, yawan nakasassu mata da suka samu inshorar tallafi ya kai miliyan 3.886, kuma miliyan 6.647 suna da tallafin kudin zaman rayuwa da na samun jiyya. A sa'i daya kuma, alkaluman da kungiyar ta fitar sun nuna cewa, daga cikin mata kimanin miliyan 5.9 dake cikin shekarunsu na aiki, fiye da miliyan 1.9 sun samu horo, kuma miliyan 2.541 sun samu aikin yi.

Shugabar kungiyar Zhang Haidi ta ce, kungiyar za ta mai da hankali kan ba da taimakon kawar da talauci, da ba da hidimar jiyya, da ba da ilmi, da kuma samar da guraben aikin yi da dai sauransu, ta yadda za a kyautata ayyukan ba da hidima ga mata nakasassu, don tabbatar da ikonsu na rayuwa da samun bunkasuwa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China