Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Al'ummar kabilar Tibet suna kokarin zaman wadata ta hanyar kiyaye muhalli
2020-10-13 15:27:08        cri

Kiyaye muhalli hanya ce mai kyau a fannin raya tattalin arziki, jihar Tibet na kokarin kyautata zaman rayuwar jama'arta, tare da kiyaye muhalli, da kafa wani tsari na dogon lokaci na kiyaye muhalli, tare da more rayuwa tare. Matakin da ya baiwa jihar damammaki masu kyau wajen samun zama mai wadata.

Yang Tsring mai shekaru 32 a duniya, na aiwatar da wani dakin kwana a gidin tsaunin Namcha Barwa. Shekarun baya-baya nan ya yi aiki a sauran wurare, amma ya yanke shawarar koma gida saboda ganin bunkasuwar garinsa, da karuwar masu bude ido a wurin. Ya nemi rancen kudi karo na farko don aiwatar da sha'aninsa.

Da farko, iyalansa na damuwa da matakin da Yang Tsring ya dauka, amma sun daina damuwa cikin sauri. Saboda Yang Tsring ya biya rabin rancen kudi da ya aro daga banki kasa da shekara daya, wanda yawansa ya kai kudin Sin RMB Yuan dubu 300.

Gwamnatin wuri kuma, ta fitar da manufar hana sare bishiya don kiyaye muhalli, da karawa mazauna wurin kwarin gwiwar dasa bishiyoyi ta hanyar samar da kudin rangwame. Mazauna wuri na samun kyauta daga indallahi, saboda matakan kiyaye muhalli da suke aiwatarwa.

Jihar Tibet mai cin gashin kanta ta hada aikin kiyaye muhalli da kyautata zaman rayuwar jama'a, tare ta hanyar ba da rangwame don kawar da kangin talauci, matakan da ya baiwa manoma da makiyaya damar samun zama mai wadata. Ya zuwa karshen shekarar 2019, jihar ta kafa wurare 278 da suke da karfin karbar masu bude ido. A watan Jarairu zuwa Yuli na bana, manoma da makiyayya a wurin da yawansu ya kai dubu 557, sun samun guraben aikin yi, kuma yawan kudin shiga da suka samu ya kai Yuan miliyan 225. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China