Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda mutanen kauyen Siji Jixiang suka samu wadata
2020-10-12 15:37:38        cri

A garin Caina na gundumar Qushui ta birnin Lhasa dake jihar Tibet, akwai wani kauye mai suna Siji Jixiang, inda dukkanin mutanen kauyan suka yi kaura zuwa nan daga wurare daban daban kafin shekaru hudu da suka gabata. Bayan da suka kaura zuwa wajen, gwamnatin wurin ta fara raya harkokin aikin gona, lamarin da ya sa, mutanen da suka kaura zuwa wajen sun samu aikin yi da kudin shiga, hakan ya sa, sun samu zaman rayuwa mai matsakaiciyar wadata.

Qiong Da wani dan kauyen ne mai shekaru 48 da haihuwa, ya ce, a halin yanzu, sun zama masu sana'ar noma, inda yanke ciyayi a wata rana guda daya, zai sa ko wanen su ya samu kudi Yuan 120. Bisa taimakon da gwamnatin wurin ta samar musu kafin shekaru 4 da suka gabata, shi da iyalinsa sun kaura zuwa wannan kauye, inda suka fara zama a gidan da gwamnatin ta samar musu ba tare da biyan kudi ba. Sa'an nan, an kuma samarwa uwargidansa aikin yi, don su samu karin kudin shiga. A halin yanzu, diyarsu tana karatu a jami'a, har an mai da iyalinsa "abin misali na garin ta fuskar neman wadata ta hanyar dukufa kan ayyuka" a shekarar 2018.

Domin samar da ayyukan yi ga manoman da suka kaura zuwa kauyen daga sauran wurare, gwamnatin kauyen Siji Jixiang ta shirya azuzuwan horaswa da samar da wasu guraben aikin yi. Har ma, ta yi amfani da kudin taimakawa masu fama da talauci wajen gina wata masana'antar kiwon zomaye da wata cibiyar shuka bishiya mai amfanin kiwon lafiya na Ganoderma.

Haka kuma, bisa goyon bayan da gwamnati ta bayar, ana raya sana'o'i daban daban a cikin kauyen, wadanda suka hada da sana'ar yawon shakatawa da sana'ar samar da kayayyakin fasaha da sauransu. kuma bisa hadin gwiwar da kauyen ya yi da kamfanonin dake kewayensa, mutanen kauye sun samu riba. Ya zuwa yanzu, gaba daya akwai mutane 1468 da suka kaura zuwa wajen, ko wanensu ya sami ribar Yuan 4900 a shekarar 2019, yayin da kudin shiga da kowanensu ya samu ya kai Yuan 11,670. (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China