Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana sun yabawa yunkurin gwamnatin kasar Sin na inganta ci gaban tattalin arziki da zamantakewar jihar Xinjiang
2020-09-30 11:23:56        cri

 

Biyo bayan dimbin kokarin da gwamnatin kasar Sin ta yi cikin sama da shekaru 10 da suka gabata, an samu gagarumin ci gaba ta fuskar raya zamantakewa da tattalin arzikin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar, inda rayuwar mutanen jihar ta ingantu.

A cewar daraktan zartaswa na cibiyar bunkasa kwarewa ta kasar Pakistan, manufar kasar Sin kan jihar Xinjiang na da ma'ana kuma ya haifar da sakamako, wadda ta tabbatar da zaman lafiya a yankin, sannan ta sauya shi ta hanyar samar da kayayyakin more rayuwa da damarmakin aikin yi da ilimi da horo.

A nata bangaren, Sonia Bressler, Bafaranshiya mai nazarin harkokin kasar Sin kuma marubuciya, ta ziyarci Xinjiang sau da dama, kuma ta wallafa tarin litattafai game da yankin.

A cewarta, manufofin gwamnati sun bada nasarar samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arzikin yankin, don haka yanayin rayuwar jama'a ya ingantu, haka ma farin cikinsu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China