Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
FAO ta yi kira da a shawo kan barnata abinci
2020-09-30 10:37:12        cri
Hukumar abinci da aikin gona ta MDD FAO, ta yi kira da a shawo kan hasara da barnata abinci. FAO wanda ta yi kiran, albarkacin ranar kasa da kasa irinta ta farko game da wayar da kan al'ummar duniya, don gane da illar barnata abinci, ta shirya taron karawa juna sani kan wannan batu, duk kuwa da fama da ake yi da matakan dakile yaduwar cutar COVID-19.

Mahalarta taron wanda ya gudana ta kafar bidiyo, sun hada da jami'ai da kwararru daga hukumar ta FAO, da jami'an shirin kare muhalli na MDD ko UNEP, da wasu jami'ai daga sauran hukumomin MDD, da ma wakilai na wasu kasashen duniya.

Mahukuntan FAOn sun ce, babban sako ga wannan taro na karawa juna sani shi ne, wajibi ne ga dukkanin sassan gwamnatoci da masu zaman kansu, da masana zuwa daidaikun mutane, su yi iya kokari wajen rage barnata ko lalata abinci, domin kaucewa babbar matsalar nan ta karancin abinci da sauran muhimman albarkatu.

Cikin jawabinsa na kaddamar da taron, babban daraktan FAO Qu Dongyu, ya bukaci da a karfafa hadin gwiwa tsakanin daukacin masu ruwa da tsaki, wajen bunkasa kirkire-kirkire masu nasaba da wannan bukata.

A nasa bangare, babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya ce bullar cutar COVID-19, ya sake fito da kalubalen da ake fuskanta a fannin samar da isasshen abinci a kasashen duniya masu yawa. Mr. Guterres ya yi kira ga gwamnatocin kasashen duniya da su kafa kudurorin rage barnata abinci, daidai da kudurorin wanzar da zaman lafiya na MDD ko SDG 12, su kuma aiwatar da tsauraran matakai na cimma wannan buri. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China