Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumomin MDD sun yi kira da a tallafawa kasashe mafiya fama da yunwa
2020-06-10 10:40:58        cri
Hukumomin MDD uku masu aikin tsara manufofi da samar da tallafin aikin gona da abinci, sun yi kira da a tallafawa kasashen duniya mafiya fama da yunwa, musamman a wannan gaba da ake shan fama da tasirin cutar numfashi ta COVID-19.

Cikin wata takaitacciyar sanarwa, hukumomin uku, wato hukumar FAO, da WFP da IFAD masu helkwata a birnin Rome na kasar Italiya, sun bayyana gazawar tsarin da ake da shi a yanzu na tallafawa al'ummun duniya, a gefe guda kuma cutar COVID-19 na kara tsananta wannan yanayi.

Sanarwar ta hakaito babban daraktan hukumar FAO Qu Dongyu na cewa, kalubalen kanfar abinci da aka lasafta, sun fi shafar yankunan dake cikin tarin matsaloli tun ma kafin bullar wannan cuta.

A bangaren sa kuwa, babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya ce bisa kiyasi, akwai kimanin mutane miliyan 49 da ka iya tsunduma cikin matsanancin talauci a wannan shekara kadai, sakamakon kalubalen cutar COVID-19.

Sanarwar ta rawaito Guterres na cewa, ya zuwa yanzu, sama da mutane miliyan 820 dake sassan duniya daban daban na fama da yunwa, duk kuwa da cewa ana noma abinci, wanda zai wadaci daukacin al'ummar duniya baki daya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China