Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
FAO: Miliyoyin mutane za su yi fama da matsalar yunwa a duniya a bana
2020-07-14 09:55:43        cri

Wani sabon rahoto kan yanayin samar da abinci da abinci mai gina jiki a duniya da aka fitar, ya yi hasashen cewa, a shekarar da ta gabata, kimanin mutane miliyan goma ne suka yi fama da matsalar yunwa, matakin da ya dakushe burin da MDD ke fatan cimmawa na kawo karshen karancin abinci da abinci mai gina jiki a duniya nan da shekarar 2030.

Rahoton da hukumar kula da abinci da aikin gona ta MDD (FAO) ta fitar jiya Litinin, ya kuma yi hasashen cewa, a shekarar 2019, kimanin mutane miliyan 690 ne suka fuskanci matsalar yunwa, karuwar mutane miliyan 10, idan aka kwatanta da shekarar 2018, adadin da ya karu da kusan mutane miliyan 60, shekaru biyar kafin lokacin da aka yi hasashe.

Sai dai rahoton bai hada da shekarar 2020 da muke ciki ba, inda ya ba da wasu kwarya kwaryar bayani, wanda ke nuna cewa, annobar COVID-19 da ta barke a duniya, tana kara haifar da illa da rashin daidaito kan tsare-tsaren samar da abinci na duniya. Rahoton ya ce, saboda wannan annoba, mutanen da za su shiga matsalar yunwa a duniya, na iya karuwa da kusan mutum miliyan 130 nan da karshen wannan shekara.

Daga karshe, rahoton ya bayyana cewa, tsanantar lamarin ta katse hanzarin duniya, na cimma nasarar burin kawo karshen yunwa da matsalar kanfan abinci, da duk wata matsalar abinci mai gina jiki nan da shekarar 2030. Wadannan manufofi dai, wani bangare na manufofin samun ci gaba mai dorewa da mambobin MDD suka amince da su a shekarar 2015. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China