Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin 'yan aware a Kamaru sun yi kira da a sake bude makarantu
2020-09-30 10:10:48        cri
A karon farko cikin shekaru 4, manyan shugabannin 'yan aware 2 a Kamaru, sun yi kira da a sake bude makarantu a yankunan kasar biyu masu fama da rikici, dake da rinjayen masu amfani da harshen Ingilishi, bayan kauracewa makarantun tsawon wasu shekaru.

A wani sakon da ya wallafa a shafin Tweeter, Mark Bareta, daya daga cikin shugabannin da ya jagoranci rajin kauracewa makarantu, ya ce yanzu matakin ba ya cikin makamansu na neman 'yanci. Don haka, ya kamata dakarun Ambazonia su kyale harkar ilimi ta ci gaba da gudana, tare da karfafa gwiwar komawa makaranta.

Shi ma sakon da ya wallafa a shafin, Eric Tataw, ya ce duba da damuwar iyaye ta neman samun tabbacin tsaron 'ya'yansu, yana kira ga mayakan Ambazonia da masu fafutuka, su hada hannu da shi a kokarin sake bude makarantu.

Tun cikin shekarar 2016, shugabannin 'yan aware suka fara rajin hana zuwa makaranta a yankunan 2 dake fama da rikici, da nufin nuna adawa da rashin adalcin da suke ikirarin ana nunawa wajen samar da ilimi ga masu amfani da harshen Ingilishi.

A cewar asusun kula da kananan yara na MDD, gangamin na kauracewa makaranta da ya shafe shekaru 4, ya hana yara sama da 800,000 zuwa makaranta.

Za a fara sabon zangon karatu a Kamaru ne daga ranar 5 ga watan Octoba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China