Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Kamaru ya yi kira da a bullo da matakai masu dorewa na samar da kudin yaki da COVID-19 ga kasashen Afrika.
2020-08-07 11:14:19        cri

Firaministan Kamaru, Joseph Dion Ngute, ya yi kira da a bullo da matakai masu dorewa na samar da kudi, daga asusun bada lamuni na duniya IMF da bankin duniya, domin taimakawa kasashen Afrika dake fama da annobar COVID-19.

Joseph Ngute ya yi wannan kira ne a farkon wani taro ta kafar bidiyo da aka yi da gwamnonin kasashen Afrika a Bankin duniya da asusun IMF.

Ya ce dole ne a amince cewa annobar za ta yi gagarumin tasiri kan kasashen Afrika. A don haka, yake kira ga IMF da bankin duniya, su dauki matakai masu dorewa da za su taimakawa Afrika samun kudade.

Ya kara da cewa, akwai bukatar kasashen Afrika su samar da wasu dabaru da za su jure kalubale da matsaloli a nan gaba, ta hanyar karfafa tsarin kiwon lafiya da sanya al'umma a gaba cikin dabarunsu na ci gaba.

Wakilai, ciki har da ministocin kudi da gwamnonin manyan bankuna daga kasashen Afrika 54, sun tattauna kan batutuwan da suka jibanci tunkarar annobar COVID-19 da dabarun farfado da kasashen nahiyar, yayin taron na yini biyu da Kamaru ta karbi bakuncinsa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China