Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi na neman kulla abota ta dindindin da kasar Cuba
2020-09-28 10:49:47        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana a yau Litinin cewa, yana matukar girmama dangantakar abota dake tsakanin Sin da Cuba, kuma a shirye yake ya taimaka wajen mayar da kasashen biyu aminai kuma 'yan uwan juna na har abada.

Xi Jinping wanda shi ne Sakatare Janar na kwamitin tsakiya na JKS, ya bayyana haka ne yayin da yake taya Raul Castro Ruz, sakatare na farko na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Cuba da kuma shugaban kasar Miguel Diaz-Canel, murnar cika shekaru 60 da kulla dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu. (Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China