Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
A shirye kasar Sin take ta taimakawa Angola a yaki da annobar COVID 19
2020-09-26 15:46:59        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce a shirye kasarsa take, ta ci gaba da taimakawa Angola iya karfinta, haka kuma za ta aike da tawagar kwararrun jami'an kiwon lafiya zuwa kasar, nan bada jimawa ba.

Yayin da yake zantawa da takwaransa na Angola, Joao Lourenco ta wayar tarho a jiya Juma'a, shugaba Xi ya ce, kasar Sin ta shiryawa bada fifiko ga musaya da kasashen Afrika bayan an ci nasarar bincike da samar da rigakafin cutar COVID-19, tare da fara amfani da shi.

A nasa bangaren, shugaban Angola Joao Lourenco, ya taya Sinawa murnar zagoyowar ranar kafuwar kasar Sin. Sannan ya godewa kasar Sin bisa taimakawa kasashen Afrika wajen yaki da cutar, ciki har da Angola.

Ya kara da bayyana fatan karfafa dangantaka da kasar Sin a fannonin da dama kamar na samar da riga kafi, tare da bayyana cewa, Angola na ba dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin muhimmanci, sannan tana goyon bayan matsayar Sin kan batutuwan da suka shafi muradunta, kuma tana maraba da samun jari daga kamfanonin kasar Sin da kara habaka dangantakar kasashen biyu a fannonin tattalin arziki da cinikayya.

Har ila yau a jiyan, shugaban na kasar Sin ya tattauna ta wayar tarho da Yoshihide Suga, sabon firaministan Japan, inda ya jadadda cewa kasashen Sin da Japan muhimman abokan huldar juna ne, sannan kuma makwabta.

A cewarsa, a shirye yake ya hada hannu da firaministan wajen taka muhimmiyar rawa da nufin inganta sabbin ci gaba ta fuskar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China