Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya jaddada gina jihar Xinjiang bisa tsarin gurguzu mai sigar musammam ta Kasar Sin a sabon zamani
2020-09-26 21:30:25        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da kokarin gina jihar Xinjiang bisa tsarin gurguzu mai sigar musammam ta kasar Sin a sabon zamani.

Xi Jinping ya bayyana haka ne yayin wani taron karawa juna sani karo na 3 kan ayyukan da suka jibanci Xinjiang, wanda ya gudana jiya Juma'a da yau Asabar a birnin Beijing.

Xi ya jaddada bukatar aiwatar da manufofin JKS yadda ya kamata dangane da gudanar da harkokin Xinjiang a sabon zamani.

Ya kuma bukaci aiwatar da nagartaccen shugabanci bisa doka da kuma yin aiki da za a dade ana mora, wanda zai raya jihar, ya kai al'ummarta ga zama tsintsiya madaurinki daya cikin lumana da ci gaba da zaman lafiya da samun ingantuwar al'adu da muhallin halittu mai kyau, ta yadda al'ummarta za su yi rayuwa da aiki cikin kwanciyar hankali. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China