Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An sake dakatar da daftarin hadin gwiwar TikTok
2020-09-26 20:15:26        cri

Dandalin yanar gizo na Tik Tok ya fidda wata sanarwa a ranar 19 ga wata cewa, babban kamfaninsa wato ByteDance, da kamfanonin kasar Amurka biyu da suka hada da Oracle da WalMart, sun cimma matsayi daya kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa da ta dace da dokokin Sin da Amurka.

A wannan rana kuma, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce, ya yarda da wannan yarjejeniya. Sa'an nan, ma'aikatar kasuwancin kasar Amurka ta jinkirta lokacin daina sabunta manhajar Tik Tok daga ranar 20 zuwa ranar 27 ga wata.

Amma, a ranar 20 ga wata, Donald Trump ya ce, idan kamfanin ByteDance ya ci gaba da rike dukkanin ikonsa kan manhajar Tik Tok, to, gwamnatin kasar Amurka ba za ta yarda da wannan yarjejeniya ba.

Dangane da wannan lamarin, kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Amurka ta taba yin amfani da hujjar tsaron kasa wajen bata ikon kamfanoni da tsarin kasuwanni, kuma kasar Sin tana adawa da matakin Amurka na aiwatar da irin wadannan harkoki. Ya ce idan kasar Amurka ta ci gaba da yin haka, tabbas, kasar Sin za ta mai da martani domin kare ikon kamfanonin kasarta yadda ya kamata. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China