Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin da ya mallaki TikTok zai shigar da gwamnatin Amurka kara
2020-08-23 16:42:23        cri

Kamfanin ByteDance, wanda ya mallakin dandalin sada zumuntar nan dake samar da bidiyo wato TikTok, ya sanar a yau Lahadi cewa, zai shigar da gwamnatin Amurka kara domin neman kare hakkinsa da moriyarsa.

A wata sanarwa da kamfanin na ByteDance ya fitar ya ce, sama da shekara guda ke nan, yana ta kokarin neman tattaunawa da gwamnatin Amurka domin samar da maslaha kan wannan batu. Amma gwamnatin Amurka ta yi watsi da dukkan hujjoji, ta bijirewa duk wasu matakan shari'a, kuma tana kokarin neman shiga cikin yarjejeniya da kamfanoni masu zaman kansu.

Sanarwar ta ce, domin tabbatar da ganin ba a yi watsi da doka ba, hakan ya sa kamfanin da abokan huldarsa suke neman a yi musu adalci, don haka zai shigar da kara a hukumance domin kiyaye moriyarsa.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China