Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta kalubalanci matakin Amurka kan rufe manhajojin WeChat da TikTok
2020-09-19 16:03:52        cri

Ma'aikatar cinikin kasar Sin MOC ta bayyana a yau Asabar cewa, tana kalubalantar yunkurin gwamnatin Amurka na dakatar da manhajojin WeChat da TikTok mallakin kamfanonin kasar Sin.

Sakamakon rashin kwararan shaidu, Amurkar tana amfani da karfin ikonta ne wajen katse hanzarin kamfanonin fasahar biyu na kasar Sin ba tare da gabatar da wasu kwararan dalilai ba, lamarin da ya yi matukar haifar da mummunan sakamako a harkokin kasuwancinsu, kana ya haifar da rashin tabbas ga masu zuba jarin kasa da kasa a kamfanonin dake Amurka, sannan matakin yana haddasa babbar illa ga sha'annin ciniki da tattalin arzikin duniya, kamar yadda sanarwar hukumar ta MOC ta fitar a shafin intanet.

Sanarwar ta bukaci Amurka ta gaggauta dakatar da nuna rashin dattakunta kuma ta mutunta dokoki da yarjejeniyoyin kasa da kasa. Kuma muddin Amurkar ta ci gaba da yin gaban kanta, kasar Sin za ta dauki kwararan matakan kare hakkokinta da moriyar kamfanonin kasarta.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China