Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
ByteDance ba zai sayarwa Microsoft ko Oracle fasahohin manhajar TikTok ba
2020-09-14 20:43:45        cri

Kamfanin ByteDance na kasar Sin ya bayyana cewa, ba zai sayarwa Microsoft ko Oracle fasahohin manhajar TikTok ba, haka kuma kamfanin ba zai baiwa duk wani kamfanin Amurka lambobin sirrin harkokin manhajar ba.

A jiya ne kamfanin Microsoft na Amurka, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, yana mai cewa, kudirinsu na sayan manhajar, zai taimaka wajen kare muradun tsaron kasar ta Amurka.

A watan da ya gabata ne, shugaba Donald Trump na Amurka, ya baiwa manhajar TikTok wa'adin zuwa gobe Talata 15 ga watan Satumba na sayar wa kamfanin Amurka ko ta fuskanci haramci, saboda abin da Amurkar ta kira, wai dalilai na tsaron kasa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China